Dakatar Da Tallafin N20,000 Ga Mabukata A Jihohin Nijeriya 4

Ministar harkokin jin kai, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta yi umarnin dakatar da aikin wasu kamfanoni guda biyu da ke rabon kudaden tallafi ga mabukata.
Wadannan kamfanoni guda biyu sun gaza wajen cika alkawarin da ke cikin kwantiragin da suka kulla da gwamnatin tarayya na rarraba kudade ga mabukata da gwamnati ta fara a wasu jihohin kasar da nufin rage radadin zaman dirshan da ake yi a gida sakamakon bullar da yaduwar Coronavirus.
Jihohin da aka dakatar da aikin raba kudaden sun hada da: Jihar Bayelsa, jihar Akwa Ibom, jihar Abia da jihar Zamfara.
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ba za ta yarda wani daga cikin kamfanonin da ta kulla yarjejeniyar raba N20,000 ga mabuka ya bata lokaci wajen isar da wannan tallafi ga wadanda aka nufa da shi ba.
Tuni dai dama ‘yan Nijeriya suke ta korafi ga yanayin tafiyar wahainiya da rabon kudin ya ke yi da kuma yadda suka ce gwamnati na gabatar da aikin rabon kudi a boye-a boye.
Kungiyoyi da daidaikun jama’a sun bukaci ministar da lalle ta wallafa sunayen mutanen da suka amfana da N20,000 na tallafin da gwamnati ta ke rabawa in dai ba akwai lauje a cikin nadi a tsarin rabon kudin ba.

Share this