Dalilin Da Yasa Ba'a Jin Wakokina A cikin Fina Finai - Hamisu Breaker

A Yanzu dai za a iya cewa a masana'antar fina-finai ta Kannywood babu wani mawaki da ya ke tashe kamar Hamisu Breaker Dorayi, domin kuwa a yanzu shi ne tauraruwar sa ta ke haskawa, dangane da haka ne a ke ganin mawakin ya sha gaban abokan sana'ar sa ta fuskar dumbun masoya, sai dai duk da tashen sa mawakin ya zo da wani Salo da ya bamban ta da sauran mawakan da ke cikin masana'antar fina-finai ta Kannywood, domin kuwa, kusan duk mawakin da ya yi tashe a cikin harkar za ka ga wakokin fim ne su ka daga shi, amma shi mawaki Hamisu Breaker sam ba a cika saka wakokin sa ma a cikin fim  ba ko me ya sa hakan?

Domin jin hanzarin sa game da hakan wakilin mu ya tattauna da shi, amma da farko ya fara da tarihin rayuwar sa kamar haka.

"Suna na Hamisu Sa'id, Yusif wanda a ka fi sa ni da Hamisu Breaker. An haife ni a unguwar Dorayi karama, Unguwar Bello. Na yi firamare a Dorayi karama Sakandare a Dorayi Babba, daga nan na dakata, amma ina da burin ci gaba da karatu da yardar Allah".

Dangane da yadda ya samu kan sa kuwa a cikin harkar waka cewa ya yi.

Cigaba da karantarwa latsa nan :

 https://www.hausaloaded.com/2020/04/dalilin-da-yasa-ba-jin-wakokina-cikin.html

Share this