Ali ArtworkFitaccen tauraron fina-finan Hausa Ali Muhammad Idris, wanda aka fi sani da Ali Artwork, ya raba kafa inda ya bude wani kamfani a jihar Kaduna da birnin tarayya Abuja mai suna AliArtWork Enterprises.

Jarumin wanda fitacce ne a cikin fina-finan Hausa na kannywood, musamman harkar barkwanci ya bude wajen ne musamman domin samar da ayyukan yi ga matasa.

Ana gudanar da abubuwa da dama a wajen, kamar sayar da motoci da bayar da su haya da hada – hadar gidaje da filaye da kuma harkokin tuntuɓa.

A shafinsa na Facebook, Ali Artwork ya wallafa wasu daga cikin hotunan buɗe wajen, inda ya gayyaci ƴan uwa da abokan arziki domin su ta ya shi murna.