Bidiyo: Ƴan ta’adda sun yi barazanar ɗauke Buhari, azabtar da fasinjojin jirgin ƙasan Abj-Kd

 


Makonni kaɗan bayan tawagar motocin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ta fuskanci hari a jihar Katsina, ƴan ta’adda sun yi barazanar ɗauke shugaban ƙasar na Najeriya. LH na wallafa

Tawagar motocin ta shugaban ƙasar tana kan hanyar ta ne ta zuwa mahaifar shugaba Buhari, Daura, kafin Sallah.

A wani bidiyo da ƴan ta’adda waɗanda suka ɗauke fasinjojin jirgin ƙasan Abuja-Kaduna suka fitar, sun yi barazanar ɗauke da kashe shugaba Buhari da gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai. Jaridar Daily Trust ta rahoto.

Ƴan ta’addan sun bugi ƙirjin cewa zasu tarwatsa ƙasar nan, su kashe ragowar fasinjojin dake a hannun su sannan su siyar da sauran.

Haka kuma a wani faifan bidiyo wanda jaridar Leadership ta fitar, ƴan ta’addan sun bayyana cewa:

Addinin Allah ya riga da ya ta shi kenan, kuma ku baku isa ku gama da Addinin Allah ba, saboda haka mu bayi ne na Allah, muna da tabbacin zai taimake mu.

Kuma ku sani shirin mu ba wai Najeriya bane kawai duniya muka sa a gaba, ka da ku ga wanan aikin (harin jirgin ƙasa) ya ta da muku hankali, daga cikin ayyukan da muka sa a gaban mu wannan bai kai komai ba.

Saboda haka mu kuma muna dogaro ne da Allahu Subhanahu Wa Ta’ala. Duk wani abun da kuke tunanin zaku tanade shi a matsayin zaku yi faɗa da addinin Allah to wallahi ku tanade shi saboda mu mun riƙe Allah.

 

Share this