Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamnatin Tarayya Zata Sanya Dokar Hana Sana’ar Acaɓa A Faɗin Ƙasar Nan

 

Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamnatin Tarayya Zata Sanya Dokar Hana Sana’ar Acaɓa A Faɗin Ƙasar Nan

Gwamnatin Tarayya ta ce tana tunanin sanya dokar hana amfani da sana’ar tuƙa babura da aka fi sani da okada.

Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya (AGF) kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ya bayyana haka a ranar Alhamis yayin da yake zantawa da manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa bayan kammala taron Majalisar Tsaro ta Kasa, da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta a fadar Shugaban kasa da ke Abuja. Jaridar Jakadiya tv na ruwaito

Ya ce bincike ya nuna cewa ana amfani da okada wajen ayyukan haƙar ma’adinai a faɗin ƙasar, kuma haramcin na iya katse hanyoyin samun kuɗaɗen ƴan ta’adda da ƴan fashi.

Ministan wanda ke tare da takwarorinsa na harkokin cikin gida da na Ƴan Sanda, Rauf Aregbesola da Mohammed Dingyadi, ya ce taron ya mayar da hankali ne kan dabarun da ƴan ta’addan ke amfani da su wajen dakatar da ayyukansu.

Ya ce akwai bukatar gwamnati ta dauki matakin saboda ‘yan ta’adda sun kaura daga hanyoyin da suka saba amfani da su wajen gudanar da ayyukansu zuwa hako ma’adinai da karbar kudin fansa.

Malami ya ce ƴan bindigar na amfani da baburan wajen motsi, yayin da hakar ma’adanai ke ba su kudaden da za su samu kudin sayen makamai.

Dangane da ko gwamnati za ta yi la’akari da illar hana babura da ayyukan hakar ma’adinai ga talakawan Najeriya da tattalin arzikin kasar, ministan ya ce gwamnatin tarayya za ta fifita bukatun kasa da na jama’a fiye da bukatun mutum daya.

A lokacin da yake jawabi, Aregbesola ya ce an yi kokari sosai wajen tattara bayanan sirri kafin harin da aka kai a Kuje Correctional Centre amma ya yi nadamar cewa babu yadda za a yi aiki da shi.

Ministan, wanda ya ce an mika rahoton farko na bincike kan harin ga shugaban kasar, ya ba da tabbacin cewa za a bayar da cikakken rahoto a karshen binciken.

Ya ce za a hukunta wadanda aka samu sun yi watsi da aikinsu.

Share this