‘Yan Ta’addan Dake Barazanar Shirin Sace Buhari, El-rufai Zasu Kawowa ‘Yan Najeriya Sauki Ne – Omokri

 

‘Yan Ta’addan Dake Barazanar Shirin Sace Buhari, El-rufai Zasu Kawowa ‘Yan Najeriya Sauki Ne – Omokri

Mai rajin kare zamantakewar al’umma, Reno Omokri ya bayyana cewa ‘yan ta’addar da ke barazanar sace shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai zasu kawo sauki ne kawai ga ‘yan Najeriya.


Jaridar Dimokuradiyya ta tuna cewa kungiyar ‘yan ta’adda a yankin Arewa maso Yamma da ta yi garkuwa da fasinjojin jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna wanda kuma a yanzu ta yi barazanar yin garkuwa da shugaban kasa Buhari da gwamna El-Rufai.


‘Yan ta’addan sun yi wannan barazanar ne a wani sabon faifan bidiyo inda aka gansu suna bulala ga wasu mutanen da suka yi garkuwa da su, musamman mazan da iftila’in ya afkawa.


Da yake mayar da martani, Omokri a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Lahadi, ya bayyana cewa ‘yan Najeriya ba za su dauki shirin ‘yan ta’adda a matsayin barazana ba sai dai kawo musu sauki.


A cewar sa, yin garkuwa da shugaban kasar na nufin sace duk matsalolin ‘yan Najeriya.


Ya rubuta cewa, “Me yasa wadannan ‘yan bindiga ke barazanar sace Buhari da El-Rufai? Ban tabbata ‘yan Najeriya sun dauki hakan a matsayin barazana ba.


“Ga ’yan Najeriya da dama, hakan zai zama annashuwa. Buhari wanda alokacin daya hau mulki ya samu da Dalar Amurka akan ₦190 yau kuma takai ₦650? Sace shi tamkar sace matsalar Najeriya ne!


“’Yan bindigar da ke barazanar sace Buhari da El-Rufai kamar yadda kungiyar Pablo Escobar ke yin barazanar sace Bola Tinubu. Menene ya shafi sauran mu? Wace tabar heroin da ta’addanci suka hade waje guda, su wanene ‘yan Najeriya da za su iya raba shi? Ina rokonka, ka bar mana jare!”

‘Yan Ta’addan Dake Barazanar Shirin Sace Buhari, El-rufai Zasu Kawowa ‘Yan Najeriya Sauki Ne – Omokri


Share this