Zulum ya fitar da Naira Miliyan 5M domin daukar karatun Yaron da ya kwafi Gadar sama da ke Maiduguri (hotuna)

Zulum ya fitar da Naira Miliyan 5M domin daukar karatun Yaron da ya kwafi Gadar sama da ke Maiduguri (hotuna)

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya sa an fitar da kuɗi har kimanin Naira miliyan 5 a matsayin tallafin karatu ga wani yaro ɗan kimanin shekara 13 da ya kwafi gadar sama da ke cikin birnin Maiduguri fadar jihar Borno. 

An gabatar da cekin kuɗin da gwamnan ya amince da shi ga wata makaranta mai zaman kan ta domin bayar da tallafin karatun ga Musa Sani, wani yaro ɗan jihar ta Borno mai shekaru 13 da haihuwa wanda ya yi amfani da taɓo wajen kwaikwayar gada ta farko da Gwamnatin jihar ta yi a shatatalen Custom Roundabout a birnin Maiduguri.

Zulum ya fitar da Naira Miliyan 5M domin daukar karatun Yaron da ya kwafi Gadar sama da ke Maiduguri (hotuna)

An dai biya waɗannan makuɗan kuɗaɗen ne ga makarantar 'Golden Olive Academy' da ke cikin Maiduguri, domin ɗaukar nauyin karatun Musa tun daga matakin aji 4 na furamare da ya ke a yanzu har zuwa kammala babbar makarantar Sakandare.

Zulum ya fitar da Naira Miliyan 5M domin daukar karatun Yaron da ya kwafi Gadar sama da ke Maiduguri (hotuna)

Musa wadda ɗan unguwar Gwange ne da ke cikin garin Maiduguri, iyayen sa masu ƙaramin ƙarfi ne da ke rayuwa ta ba yabo ba fallasa. 

Ya fara makarantar furamaren sa ne a wata makarantar al'umma ta Gwange, in da har ya kai aji 3 kamin Hukumar Gudanarwar kamfanin gine-gine na Ronches su ɗauki nauyin karatun sa a watannin baya ta hanyar mayar da shi makarantar kuɗi da ya ke a yanzu, biyo bayan yaduwar hotunan sa a shafukan Sada Zumunta na zamani. 

Zulum ya fitar da Naira Miliyan 5M domin daukar karatun Yaron da ya kwafi Gadar sama da ke Maiduguri (hotuna)

Musa dai ya ɗauki hankalin Gwamna Zulum ne bayan da ya yi amfani da taɓo wajen ƙera irin gadar sama da gwamnatin Zulum ɗin ta gina a Maiduguri wadda Shugaba Muhammadu Buhari ya ƙaddamar a Maiduguri, a watan Disambar 2021.

Gwamna Zulum wadda ya yi matuƙar mamakin hazaƙar yaron, ya haɗu da iyayen shi, hakan kuma ya ba shi damar ba shi tallafin karatu don ƙarfafa shi ya bunkasa basirar sa.

Gwamnan dai ya umarci Asusun Tallafawa Ilimi na Jihar Borno (ETF) da aiwatar da wannan aiki na ɗaukar nauyin karatun yaro Musa.

Shugabar Hukumar ETF Farfesa Hauwa Biu, ta gabatar da cekin Naira Miliyan Biyar da Dubu Ashirin da Tara (N5,029,000) na kuɗin da aka biya ɗin ga makaranta mai zaman kan ta da Musa ke karatu a yanzu haka.

Zulum ya fitar da Naira Miliyan 5M domin daukar karatun Yaron da ya kwafi Gadar sama da ke Maiduguri (hotuna)

Farfesa Biu, ta godewa Gwamna Zulum bisa wannan ƙoƙari, sannan ta buƙaci yaron da ya maida hankali kan karatun sa, domin ya zama abun alfahari ga al'ummar jihar Borno da ma gwamnan.

Idan za a tuna dai, labari da hotunan gadar da Musa ya kwaikwaya ta fara bayyane a watannin baya a cikin wannan shekara ta 2022 a sahar Facebook wadda shafin jaridar Rariya ta fara yaɗawa. Kuma bayan da ya ƙera ta a gidan su, mahaifiyar sa ta rushe ta a dalilin cika mata gida da cincirindon yara su ke yi don kallo. Kamin daga bisani kamfanin da ya gina ainahin gadar da Musa ya kwaikwaya, wato Ronches Construction Company LTD ya ga wannan bajinta ta sa, ya kuma karrama shi tare da ɗaukar nauyin karatun na shi.

Ahmad A. Umar 

Nagudu TV

Share this