Allah Sarki Al’umma Sun Hada Kudi Naira N744,115.00 ga wata Budurwa Mai Talla da Akaga Ta Tsaya tana Cikin Kasuwa.

Allah Sarki Al’umma Sun Hada Kudi Naira N744,115.00 ga wata Budurwa Mai Talla da Akaga Ta Tsaya tana Cikin Kasuwa

A tallafin Da Ake hadawa Hauwa’u Daga shekaran jiya zuwa yanzu an Samu gudunmowar jimillar kudi Naira dubu dari bakwai Da arba’in da hudu Da Naira dari daya da Goma sha biyar 744,115.00

Idan baku manta ba a kwanakin baya Jaridar Amintacciya ta rawaito muku cewa, wani mai anfani da kafafen Sada Zumunta Abdulmudallib Hamza Kibiya ne ya hangi wannan baiwar Allah tana Sallah dai dai lokacin da take yawon talla, ganin haka yasa ya dora a shafin sa na Facebook.

Allah Sarki Al’umma Sun Hada Kudi Naira N744,115.00 ga wata Budurwa Mai Talla da Akaga Ta Tsaya tana Cikin Kasuwa.

Sakamakon haka ne yasa labarin matashiyar ya zagaye kafafen Sada Zumunta inda jama’a da dama ke neman yadda za’a gano inda take.

Cikin ikon Allah kamar yadda ya bayyana, a yau ne ya sami haɗuwa da wannan baiwar Allahn wacce tai Sallah a kasuwa Bayan kwashe kwanaki 6 ana Nemanta.

Kamar yadda ya bayyana yanzu haka zai tafi da ita gidansu, domin suyi Magana da iyayenta.

Allah ya Sakawa Kowa Da Alkhairi, Kuma Har yanzu Dai kofa a bude take, Allah ya Bada ikon taimakawa.

Share this