Idan na sauka daga mulki ba wanda zai min ƙazafi da satar kuɗin talakawa, in ji Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake jaddada ƙudurinsa na bauta wa Allah da Nijeriya har zuwa ranar da zai sauka da ga mulki da kuma bayan nan.

Idan na sauka daga mulki ba wanda zai min ƙazafi da satar kuɗin talakawa, in ji Buhari


Majiyarmu tajiyo daga Daily Nigerian Hausa Buhari ya ce babu wanda zai yi masa kazafi a satar kan dukiyar talakawa da yin arziki ta hanyar kuɗin sata lokacin da ya ke kan mulki.


Femi Adesina, a wata sanarwa da ya fitar a yau Talata, ya ce Buhari na magana ne a wajen wata liyafa da aka shirya a daren jiya Litinin a Damaturu, babban birnin Yobe.


A cewar shugaban, babu wanda zai iya yi masa kazafi da tara kazamar dukiya da kuma kuɗin haram a lokacin da yake kan mulki, yana mai cewa ”Bani da inci daya a wajen Najeriya”.


Ya shawarci ‘yan Nijeriya da su kasance masu kishin kasa, yana mai cewa ‘’Kamar yadda na fada sama da shekaru 30 da suka gabata, ba mu da wata kasa face Najeriya, dole ne mu tsaya a nan mu gyara ta tare.’’


Buhari ya ce babban kalubalen tsaro da gwamnatinsa ta gada kusan shekaru takwas da suka gabata shi ne barazanar ta’addanci da ta mamaye ta.


Sai dai ya bayyana jin dadinsa yadda al’amura su ke komawa kamar yadda aka saba a Jihohin Arewa maso Gabashin Nijeriya.

Share this