An buɗe bikin nuna fina-finai na duniya a Saudiyya (Hotuna)


An buɗe bikin nuna fina-finai na duniya a Saudiyya (Hotuna)


Za a buɗe bikin fina-finai na farko a ƙasar Saudiyya a birnin Jeddah - kasa da shekaru hudu da ɗage haramcin nuna fina-finai a ƙasar.


Bikin fina-finai a ƙasar zai gudana ne na tsawon kwanaki 10 inda za nuna fina-finai138 daga sassan duniya.


Bbchausa na ruwaito za a karrama darakta mace ta farko a Saudiyya Haifa al-Mansour - wacce ta fara fim din Wadjda da ta lashe kyauta.


Manufar bikin ita ce bunƙasa masana'antar fina-finai a ƙasar Saudiyya - ta fuskar shirya fina-finai da kuma kasuwarsu da nunawa a sinima da aka buɗe tun shekarar 2018.

Share this