Shahararren mai wa'azin Boko Haram Alhaji Ari-Difinoma ya mika wuya ga sojojin Najeriya

 

Shahararren mai wa'azin Boko Haram Alhaji Ari-Difinoma ya mika wuya ga sojojin Najeriya

Aliyu Samba


Wani fitaccen mai wa’azi kuma babba a kungiyar Jama’at Ahl as-Sunnah lid-Da’wah wa’l-Jihād (JAS), kungiyar ta’addancin Boko Haram, Alhaji Ari-Difinoma, ya mika wuya ga rundunar sojojin Nijeriya.


An tattaro cewa Ari-Difinoma, ya mika kansa ga sojojin 21 Special Armored Brigade Bama, dake gudanar da atisayen Operation Hadin Kai, a ranar 16 ga Mayu, 2022.


Majiyar mu ta tattaro cewa an fatattaki Ari-Difinoma, daga maboyarsa biyo bayan ci gaba da ruwan bama-bamai da dakarun Operation Hadin Kai suka yi.


Sauran dalilan miƙa wuyan nasa sun hada da rikicin da ya barke tsakanin kungiyar Boko Haram da bangaren da ke adawa da ita, kungiyar IS da ke yammacin Afirka (ISWAP).


ISWAP ta kaddamar da harin ba-zata a kan 'yan Boko Haram a garin Ukuba, sansanin da sojojin Najeriya suka yi ta bata kashi da su, amma 'yan ta'addar suka sake mamayewa, lamarin da ya tilastawa 'yan Boko Haram guduwa daga yankin.


Majiyar ta bayyana cewa Ari-Difinoma da sauran yan Boko Haram sun gudu sun buya a wani karamin kauye da ke kauyen Mantari, a cikin yankin karamar hukumar Bama, amma yunwa da ruwan harsashin bindiga da sojojin Najeriya suka yi musu ya tilasta musu ficewa daga maboyarsu.


Alhaji Ari-Difinoma, wanda dan asalin garin Monguno ne a jihar Borno kuma ya rike daya daga cikin makarantar koyar da Tsageranci da ke sansanin Ukuba da ke dajin Sambisa karkashin Darul-Qur’ani, ya dauki yara da matasa da dama aiki ta hanyar koyar da akidar tsageru a shekaru 10 baya. 


Idan ba a manta ba, ‘yan ta’addar Boko Haram/ISWAP sama da 52,000 da suka hada da mayaka, sun mika wuya ga sojojin Najeriya.


📷Zagazola

Share this