Bayan da nayi rubutu me wannan suna kashi na farko, sai na fahimci ashe mazan da suke cikin irin wannan kalubale na soyayya da irin wadancan mata da muka ambata suna da yawan gaske, kuma tabbas hakan yana matuƙar ci musu tuwo a kwarya, domin babu wanda zaiso ace kullum shine yake nema, amman shi ba za'a nemesa ba, kullum shine yake kira, amman shi ba za'a kirasa ba, kullum shine cikin furta kalaman soyayya, amman shi har yanzu ya kasa fahimtar shin ana son shi ko kuma ba'a son shi?
Hakan sai yasa nace bara na kara haskawa yan uwana samari wani hasken, doriya akan na farko, watakila su fita daga cikin duhun da suke a ciki na rashin sanin inda matsalar Abar Kaunar su take!
ABU NA FARKO yana dakyau ka sani, mata masu WUYAR SHA'ANI A SOYAYYA kala 3 ne, kuma insha Allah yanzu za muyi bayanin kowacce daga ciki,
1- MACE MAI ZURFIN CIKI: Tabbas mace me zurfin ciki tana da wuyar sha'ani a soyayya, domin duk irin son da take maka, ba zata taba sakin jiki tayi ta nuna maka soyayya ba, saidai tayi ta boye komai a ranta, amman a bayan idonka za ta saki jiki tayi ta bada labarin ka, da irin son da take maka, saidai duk da zurfin cikin da take dashi tana iya baka hakuri a duk lokacin da ta fahimci ta yi maka laifi.
2- MACE ME TSANANIN KUNYA: Kunya abar so ce ga kowacce mace, domin ita din ado ce ga kowacce mace, saidai idan tayi yawa ba zata baka damar da za ka mori soyayyar ka da Abar Kaunarka ba, Mace me tsananin kunya ko hada ido dakai ba za ta iya yi ba, duk firar da za kuyi saidai idonta na kallon kasa ko kuma yana kallon wani wurin, duk irin son da take maka itama ba zata nuna maka ba, saidai ka dinga samun labarin irin son da take yi maka daga wurin makusantanta.
3- MACE ME GIRMAN KAI: Dagaske ne akwai mata masu girman kai sosai, suna son ka, amman ba za su nuna suna son ka ba, saboda kada ka raina su, irinsu ne ko laifi suka yi maka ba zasu taba baka hakuri ba, zaka iya kwashe sama da wata guda kana kiranta a waya kullum, amman idan ka daina kiranta na tsawon kwanaki 3 wallahi ba za ta kira ka taji ko lafiya ba? Saboda girman kanta bazai barta ba, kuma faa tare da hakan tana sonka!
Don haka kafin ka fara korafi akan budurwar ka, yana dakyau ka fara nemo ajin da take ciki a cikin waɗannan ajujuwa guda 3.
Insha Allah a rubutu na gaba, za mu yi bayanin yanda zaka tafiyar da kowacce daga cikin su.
~ Abubakar Haruna Sani.