Mace me wuyar sha'ani A soyayya

 

Mace me wuyar sha'ani A soyayya

Tana Sonka, amman duk rintsi ba zata iya furta maka tana sonka ba, koda kuwa a rubuce ne, idan kayi mata kalaman soyayyar da taji dadinsu, amsar da zaka samu daga gareta shine: TA GODE,


Tana damuwa idan baka kirata ba, amman duk damuwar da zata yi ba zata dauki wayarta tace ita bari ta kira ka ba, dole saidai idan kaine ka kirata tukunna, 


Yawan fara'a bai dameta ba idan kuna tare, amman idan wata a cikin kawayenta tayi mata maganarka, yanzu zaka ga fuskarta ta cika da annuri,


Saboda tsananin zurfin cikinta tafi karfin ta baka hakuri idan tayi maka laifi, saidai kayi fushin ka gama, ka sakko don kanka, sannan ka dawo gareta kuci gaba daga inda kuka tsaya, kuma a zuciyar ta tana son ta baka hakurin, amman ba zata iyaba, hakan kamar zubewar kima ne a gareta, (a wasu lokutan ma ba zata yarda tayi maka laifin ba)


Idan za kayi shekara baka je gidansu ba, ba zata tambayeka yaushe zaka je ba? Saidai kai don kanka kace da ita zaka zo rana kaza, idan taga dama tace dakai ma ranar bata nan,


Dole kaine zaka bukaci tura iyayenka gidansu domin ayi maganar aure, shima sai kunyi fama kafin ta yarda ka tura din, amman ita da kanta ba zata taba cewa dakai ka turo ba,


Akwai irin waɗannan yan matan da yawan gaske a wannan zamanin, sun yawaita sosai, duk wanda Allah ya hadashi soyayya da irinsu, tabbas sai ya kasance me tsananin hakuri da juriya, domin duk yanda kaso canzasu, ba zasu tab'a canzuwa ba, saboda halittarsu ce a haka, 


Idan kuwa Allah ya kaddara rabuwa ta shiga tsakanin ka dasu kafin aure, anan suke shiga mawuyacin halin da babu waɗanda ke sani sai na kusa dasu, a sannan suke gane girman soyayyar da suke maka, a sannan suke kuka tare da zubda hawayen rashinka da suka yi, a sannan suke jin ina maa ka dawo garesu domin su nuna maka kulawa da soyayyar da suka kasa baka a baya, saidai kash! Bakin alkalami ya riga da ya bushe!


Idan har halittar ki a haka take, to kiyi iyakar bakin kokarinki domin ganin kin canza daga wannan dabiar, domin dabia ce wadda dukkan wanda yake sonki baya so, kowanne mai sonki babban burinsa shine samun soyayya kamar yanda yake nuna miki, ba kowa ke iya jure wancan tsananin zurfin cikin daga wadda yake so  ba!


SHIN KA TAB'A HADUWA DA IRIN WANNAN MACEN???


~ Abubakar Haruna Sani

Share this